Dakatar da tattara sakamakon zabe: Anyi zanga-zanga kan umurnin kotu a Bauchi

Dakatar da tattara sakamakon zabe: Anyi zanga-zanga kan umurnin kotu a Bauchi

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zanga-zangar Allah wadai da hukuncin tsayar da ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihar Bauchi da kotu ta bayar.

Wadanda ke zanga-zangar sun bayyana cewa basu aminta da yunkurin take masu hakki da ake shirin yi ba.

Masu zanga-zangar dai sun mamaye daidai shingen da jami’an tsaro suka sanya a hanyoyin shiga ofishin INEC da ke Bauchi suna masu rera wakoki daban-daban da ke cewa su Kaura suke so ba Gwamna Muhammad Abubakar ba.

Dakatar da tattara sakamakon zaben: Anyi zanga-zanga kan umurnin kotu a Bauchi
Dakatar da tattara sakamakon zaben: Anyi zanga-zanga kan umurnin kotu a Bauchi
Asali: UGC

Mata da matasa ne dai suka fi yawa a cikin masu shiga Zanga-Zangar, a gefe guda kuma jami’an tsaro sun kara karfi sosai domin baiwa INEC din kariya.

A halin da ake ciki, mun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da ci gaba da karbar sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi, wanda ta fara karba a ranar Talata, 19 ga watan Maris, 2019.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Wike ya tura ‘Yan daba su ka sace mu – Inji Chikordi Dike

Kamar yadda Channels TV ta wallafa, hukumar ta yanke wannan hukunci ne bayan da wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar zaben da ta tsayar da karbar zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar ta Bauchi.

A baya bayan nan, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa; Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC daga ci gaba da karbar sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi wanda ya gudana a ranar 9 ga watan Maris.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel