Yadda 'yan Boko Haram suka kwashi kashin su a hannu yayin artabu da sojin Najeriya a Michika

Yadda 'yan Boko Haram suka kwashi kashin su a hannu yayin artabu da sojin Najeriya a Michika

Rundunar sojin Najeriya ta bayar da labarin yadda ta dakarun ta suka yi kasa-kasa da 'yan ta'addan Boko Haram a da suka so kai farmaki garin Michika na jihar Adamawa dake Arewa maso yammacin Najeriya ranar Litinin din da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar kuma jami'in hulda da jama'ar ta, Kanal Musa Sagir ne ya bada wannan labarin a cikin wata sanarwar manema labarai da sanyawa hannu ya kuma rabawa 'yan jarida a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Yadda 'yan Boko Haram suka kwashi kashin su a hannu yayin artabu da sojin Najeriya a Michika
Yadda 'yan Boko Haram suka kwashi kashin su a hannu yayin artabu da sojin Najeriya a Michika
Asali: Twitter

KU KARANTA: Najeriya na kashe $5,000,000 wajen shigowa da man ja

A cewar sa, 'yan Boko Haram da farkon daren Litinin din da ta gabata sun so su kai farmaki a kauyen Michika amma sai Allah ya tona asirin su yayin da 'yan bangar dake a garin suka gan su suka kuma fadawa sojojin bataliya ta 115 dake a garin Lassa, jihar Borno.

Ya cigaba da cewa ba tare da wata-wata ba sai sojojin nan suka yi shiri suka zagaye 'yan ta'addan suka yi masu kwanton bauna sannan suka kashe su. Wasu daga cikin su kuma da suka so guduwa sai aka kama su kuma yanzu haka suna hannu.

Sanarwar ta cigaba da cewa sojojin haka zalika sun samu nasarar kwace mota kirar Ford da wasu motocin 2 kirar Toyota Starlet shakare da kayayyakin abinc da moshina da dai sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel