Udoma ya bayyana yadda gwamnatin Nigeria ta tsara biyan mafi karancin albashi

Udoma ya bayyana yadda gwamnatin Nigeria ta tsara biyan mafi karancin albashi

- Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Sanata Udo Udoma, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba yiyuwa sake fasalin kudaden da kasar ke samu daga haraji (VAT)

- Sanata Udo Udoma ya ce za a kara bunkasa bangaren harajin kasar na VAT da nufin samun isassun kudaden da zasu bada damar biyan mafi karancin albashi a kasar

- Ministan ya kara da cewa kwamitin mashawarta kan mafi karancin albashi za su gabatarwa Buhari rahoton da suka tattara a wannan makon

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Sanata Udo Udoma, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba yiyuwa sake fasalin kudaden da kasar ke samu daga haraji (VAT), da nufin samun isassun kudaden da zasu bada damar biyan mafi karancin albashi a kasar.

Ministan ya bayyana hakan a ranar Talata a lokacin da ya gurfana gaban wani kwamin majalisar dattijai kan harkokin kudade, bisa jagorancin Sanata John Enoh.

A cewar Mr Udoma, tsarin samun kudaden shiga cikin lalitar kasar ta VAT na daga cikin tsari mafi karanci da ke kawowa kasar kudaden shiga a yanzu, wanda kuma idan aka bunkasa shi zai iya wadatar da mafi karancin albashin kasar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Shugaban kasar Khazak ya yi murabus bayan shafe shekaru 29 yana mulki

Udoma ya bayyana yadda gwamnatin Nigeria ta tsara biyan mafi karancin albashi
Udoma ya bayyana yadda gwamnatin Nigeria ta tsara biyan mafi karancin albashi
Asali: Depositphotos

"Muna daf da zuwa majalisar dattijai saboda akwai yiyuwar sake fasalin wasu muhimman bangarori musamman bangaren VAT, domin samun kudaden mafi karancin albashi da zaran an amince," a cewar sa.

Ministan ya kara da cewa kwamitin mashawarta kan mafi karancin albashi da fadar shugaban kasa ta kafa, za su gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari rahoton da suka tattara a wannan makon.

A cewar sa: "Mafi karancin albashin da yake kan aiki yanzu na N18,000 ya yi kadan gaskiya. Yana zama wahala ga ma'aikata su rayi da wannan albashi. Shugaban kasa ya amince da sake fasalin mafi karancin albashin, amma abun dubawar shi ne, in har za mu kara albashin to ya zama tilas mu nemi hanyoyin samun kudaden biyan karin albashin."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel