'Yan Majalisun Arewa ta tsakiya sun bukaci a basu kurejar Kakakin Majalisa

'Yan Majalisun Arewa ta tsakiya sun bukaci a basu kurejar Kakakin Majalisa

- 'Yan majalisar wakilai na tarayya na yankin Arewa ta Tsakiya sun bukaci a baiwa yankin shugbancin majalisar a wannan karo

- 'Yan majalisar sun ce duba da irin muhimmiyar rawar da yankin ta taka yayin zabe, ya dace a ce a basu shugbancin majalisar

- 'Yan majalisar na arewa ta tsakiyar karkashin jagorancin John Dyegh sun ce sauran yankunan kasar sunyi shugbancin saboda haka ya dace a basu su dana

'Yan majalisar wakilai daga arewa ta tsakiya sun fara shirin karbar kujerar shugabancin majalisa
'Yan majalisar wakilai daga arewa ta tsakiya sun fara shirin karbar kujerar shugabancin majalisa
Asali: Depositphotos

Wakilan yankin arewa ta tsakiya a majalisa 'yan jam'iyyar APC sun bukaci a bayar da shugabancin Majalisar ga dan yankin saboda irin gudummuwar da su ka bayar wurin samun nasarar da jamiyyar ta yi.

John Dyegh tare da goyon bayan wakilai na yankin ne ya bayyana hakan a ranar talata.

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

A cewar sa, tunda arewa maso yamma da kudu maso yamma sun fitar da shugan kasa da mataimaki, abun da ya ke adalci da daidaito shi ne a ba wa sauran yankunnan mukamai ma su maiko a majalisu.

Ya yaba da irin kokarin da jam'iyyar ke yi na ganin ta tabbatar da adalci wurin raba manyan mukamai don tabbatar da adalci da hadin kai. Don haka ne ya sakankance jamiyyya za ta saurari bukatar su.

Ya kuma yi tsokaci game da yadda zaben shuwagabannin majalisun da su ka gabata ya kawo cikas da rabuwar kai a majalisar. Don haka ne ya yi kira da a kula sosai don kar a koma gidan jiya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel