Zaben 2019 a Najeriya mummunan labari ne ga dimokradiyya – Amurka

Zaben 2019 a Najeriya mummunan labari ne ga dimokradiyya – Amurka

John Campbell, tsohon jakadan kasar Amurka a Najeriya, ya ce zabukan da aka gudanar a Najeriya a shekarar na, 2019, mummunan labara ne ga dimokradiyya.

Campbell, ma’aikaci a ofishin jakadancin kasar Amurka daga shekarar 1975 zuwa 2007, ya bayyana cewar an samu karancin fitowar ma su kada kuri’a da kuma sahihan zarge-zargen tafka magudi lokacin zabukan shekarar 2019.

A wata takardar sharhi a kan zaben Najeriya da ya gabatar a ofishin harkokin kasashen ketare na kasar Amurka da ke birnin Washington DC, Campbell, wanda ya taba rubuta littafi a kan Najeriya mai taken “Nigeria: what everyone needs to know,” ya bayyana cewar zai yi matukar wuya dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasara a karar da ya shigar kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa.

Zaben 2019 a Najeriya mummunan labari ne ga dimokradiyya – Amurka
Atiku da Campbell
Asali: Facebook

Tazarar kuri’u miliyan hudu da hukumar zabe ta bayyana shugaba Buhari ya bawa Atiku ta yi yawan da ba zai saka wata kotu ta soke sakamakon zaben ba,” a cewar Campbell.

Kazalika ya bayyana cewar an samu ci baya a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 idan aka kwatanta shi da na shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Maimaita zabe: Masoya Ganduje sun yi zanga-zanga a kan kwamishinan 'yan sanda 'Singham'

A jiya, Litinin, ne Atiku da jam'iyyar PDP su ka shigar da karar kalubalantar nasarar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shugaba Buhari ya samu a zaben da aka gudanar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Kafin shigar da karar ta jiya, Atiku da PDP sun samu sahalewar kotu na ba su damar gudanar da bincike a kan kayan aikin zabe da aka yi amfani da su yayin zaben shugaban kasa.

Sai dai har yanzu INEC ba ta bawa Atiku da PDP damar gudanar da bincike a kan kayan aikin zaben ba duk da hukuncin da kotu ta yanke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel