Bayan ganawar sa’o’i 3 da Buhari, shugabannin tsaro sun ki cewa uffan

Bayan ganawar sa’o’i 3 da Buhari, shugabannin tsaro sun ki cewa uffan

Bayan ganawar sirri na tsawon sa’o’i uku da ya wakana a tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannintsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro a fadar Shugaban kasa, Abuja babu ko mutum guda daga cikinsu da ya yarda yayi sharhi akan abunda ya wakana.

Sabanin ganawar da sukan yi a baya inda Sufeto Janar na Yan sanda, Mohammed Adamu ke takaitaccen jawabi ga manema labarai, babu ko guda da ya afku a wannan karon, wadanda suka halarcin taron sun fice ne baki dayansu.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai; Shugaban sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas da kuma Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshall Abubakar Sadique.

Bayan ganawar sa’o’i 3 da Buhari, shugabannin tsaro sun ki cewa uffan

Bayan ganawar sa’o’i 3 da Buhari, shugabannin tsaro sun ki cewa uffan
Source: Twitter

Sauran sun hada da mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Monguno; ministan tsaro, Mansur Dan- Ali; ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahaman Dambazau; Shugaban hukumar liken asiri na kasa, Ahmed Abubakar; mukaddashin Shugaban yan sanda, Mohammed Adamu da kuma darakta janar na yan sandan farin kaya, Yusuf Magaji Bichi.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ma ya halarci ganawar.

KU KARANTA KUMA: Kano: Na riga na kafa majalisar Abba gida-gida - Kwankwaso

A lokacin da aka tunkare shi domin yayi martini akan zargin hukumar zabe mai zaman kanta kan rawar ganin da rundunar soji ta taka a jihar Rivers wanda ya kai ga tarwatsa tsarin zaben, Buratai wanda kan yi Magana ga manema labarai, yayi murmushi sannan yace “ku jira IG”.

Amma IGP Adamu bai yi Magana ba shima. Kawai cewa yayi “ babu wani bayani.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel