Gwamnatin tarayya ta saka sharadin biyan sabon albashi na N30,000

Gwamnatin tarayya ta saka sharadin biyan sabon albashi na N30,000

Ministan Kasafin Kudi da Tsatsare na Kasa Sanata Udo Udoma ya ce gwamnatin tarayya tana tunanin kara harajin kayan masarufi domin ta samu ikon biyan sabon albashi mafi karanci na N30,000.

Udoma ya fadi hakan ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban kwamitin kudi majalisar dattawa.

Ministan ya kuma shaidawa kwamitin karkashin jagorancin Sanata John Owan-Enoh cewa kwamitin kwararu masu bayar da shawara a kan albashin mafi karanci za ta mika rahoton ta ga shugaba Muhammadu Buhari a cikin wannan makon.

Sabon albashi: FG ta bayar da sharrudan biyan N30,000 bayan amincewar majalisa
Sabon albashi: FG ta bayar da sharrudan biyan N30,000 bayan amincewar majalisa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Maimaita zabe a Kano: Ku zargi Kwankwaso idan aka samu tashin hankali - APC

Ya ce, "Albashi mafi karanci na N18,000 da ake biyan ma'aikata ya yi kadan sosai. Yana da matukar wahala ma'aikata su tafiyar da rayuwar su a kan wannan kudin.

"Shugaban kasa yana goyon bayan a sake duba batun albashin amma duk da hakan ya dace mu san cewa za mu iya biyan albashin.

"Saboda haka ne yasa muka zo wurin ku a majalisa domin akwai yiwuwar a yi wasu sauye-sauye musamman a harajin kayan masarufi saboda mu samu ikon cigaba da biyan albashin da zarar an zartas da shi."

A yau Talata ne kuma majalisar dattawar ta amince da N30,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci.

An cimma wannan matsayar ne bayan kwamitin wucin gadi na sabon albashin mafi karanci karkashin Sanata Francis Alimikhena ta mika rahoton ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel