Hatsarin jirgi: Majalisar dattawa ta yi jimamin mutuwar 'yan Najeriyar da suka mutu

Hatsarin jirgi: Majalisar dattawa ta yi jimamin mutuwar 'yan Najeriyar da suka mutu

Sanatocin Najeriya a majalisar dattawan kasar a ranar Talata tayi jimamin mutuwar wasu 'yan Najeriya a hatsarin jirgin saman Itofiya da ya rutsa da su mai lamba ET 302 a satin da yagabata ciki hadda wani fitaccen Farfesa.

Farfesa Pius Adesanmi na adabi a wata jami'ar kasar Kanada kuma dan asalin kasar Najeriya da Mista Abiodun Bashuwa na cikin manyan 'yan Najeriya da hatsarin ya rutsa da su cikin jirgin mai kirar Boeing 737.

Hatsarin jirgi: Majalisar dattawa ta yi jimamin mutuwar 'yan Najeriyar da suka mutu
Hatsarin jirgi: Majalisar dattawa ta yi jimamin mutuwar 'yan Najeriyar da suka mutu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin APC na shirin tsige gwamnan Imo

Sanatocin dai a yayin jimamin na su sun yi shiru na minta daya domin girmamawa ga gawar mamatan sannan kuma suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara tsaurara matakai domin samun yanayi mai cike da tabbas a harkokin sufurin kasar baki daya.

A wani labarin kuma, hukumar gwamnatin tarayya dake yaki da masu laifuka da suka jibanci damfara watau Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPS) ta shirya kwace wasu filaye da gine-gine da suka kai darajar Naira biliyan 4.8 daga kamfanoni akalla 30.

Hukumar ta ICPC ta ce za ta kwace kadarorin ne daga hannun masu su saboda karar da aka kai masu na kin biyan harajin da ya kamata su biya na tsawon lokaci kamar dai yadda doka ta tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel