Kisan Kajuru: 'Yan kungiyar kudancin Kaduna sunyi zanga-zanga a Abuja, hoto

Kisan Kajuru: 'Yan kungiyar kudancin Kaduna sunyi zanga-zanga a Abuja, hoto

Wata hadakar kungiyoyi na yankin kudancin jihar Kaduna sunyi zanga-zanga a kan harin da aka kai a karamar hukumar Kajatru na jihar da ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

An gudanar da zanga-zangan ne a dandalin Unity Fountain da ke babban birnin tarayya Abuja domin nuna damuwar su a kan hare-haren da ake kaiwa a garin kamar yadda Channels TV ya ruwaito.

Masu zanga-zangan sun zargi gwamna Nasir El-Rufai na jihar da lafin harzuka kai harin ramuwar gayya kuma sun bukaci a sako shugbanin su da hukumomin tsaro ke rike da su.

DUBA WANNAN: Maimaita zabe a Kano: Ku zargi Kwankwaso idan aka samu tashin hankali - APC

'Yan kungiyar kudancin Kaduna sunyi zanga-zanga a Abuja, hoto
'Yan kungiyar kudancin Kaduna yayin da suka zanga-zanga a Abuja domin a sako shugabaninsu
Asali: Twitter

Kisan Kajuru: 'Yan kungiyar kudancin Kaduna sunyi zanga-zanga a Abuja, hoto
Matasan kudancin Kaduna dauke da takardu da hotuna yayin zanga-zangan da suka gudanar a Unity Fountain a Abuja domin neman a sako shugabaninsu
Asali: Twitter

A cikin kwana-kwanan ne 'yan bindiga suka rika kai hari a garin Kajuru da ke jihar Kaduna inda suka kashe mutane da dama sunnan mutane 30,000 sun rasa muhallinsu.

An dade ana kai hare-hare a wasu garuruwa da ke yankin kudancin Kaduna tun farkon wannan shekarar da ya janyo gaba da rikici tsakanin 'yan kabilar Adara da Fulani da ke zaune a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel