In da ranka ka sha kallo: Uwa ta halaka diyarta yar shekara 3 bayan Mijinta ya saketa

In da ranka ka sha kallo: Uwa ta halaka diyarta yar shekara 3 bayan Mijinta ya saketa

Wata kotu dake zamanta a garin Winchester na kasar Ingila ta yanke ma wata mata mai shekaru 36 hukuncin daurin rai da rai bayan ta kamata da laifin kashe diyarta yar shekara 3 da gangan, kawai don mahaifin yarinyar ya saketa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matar mai suna Claire Colebourn ta halaka diyarta Bethan Colebourn ne ta hanyar tsomata a cikin ruwan baho a gidansu har sai da tace a ga garinku nan, sa’annan itama tayi kokarin kashe kanta, shekarar 2017.

KU KARANTA: Hamid Ali ya karrama jami’in kwastam da yayi watsi da tayin cin hancin N152m

In da ranka ka sha kallo: Uwa ta halaka diyarta yar shekara 3 bayan Mijinta ya saketa
Bethan da Claire
Asali: UGC

Alkalin kotun, Johannah Cutts ta bayyana cewa kamata yayi Claire ta nemi agaji daga hukuma bayan ta samu kanta cikin mawuyacin hali biyo bayan mutuwar aurenta, a maimakon kashe diyarta da tayi, wanda bata san hawa ba, bata san sauka ba.

“Duk irin damuwar da kika shiga, bamu ga wata hujjar ciwon hauka a tattare dake ba, ke uwace a wajen Bethan, ke ya kamata ki dauki alhakin kulawa da ita, amma kika kasheta don ki bakanta ma tsohon mijinki rai.” Inji Alkalin.

Shima mahaifin Bethan, Michael Colebourn ya bayyana damuwarsa da bakin cikinsa bisa mutuwar diyarsa, inda yayi juyayin rashinta, tare da tsananin halin kewarta da ya shiga a yanzu, musamman yadda yace sun shaku da juna.

A nata bangaren, Claire ta bayyana cewa tsohon Mijinta Michael ne ya jefata cikin wannan mawayucin hali tun bayan daya yi watsi dasu a ranar 7 ga watan Satumbar shekarar 2017, kuma ya tare da uwardakinsa a waje aiki, bai kara komawa gida ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel