Maimaita zabe a Kano: Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga, hotuna

Maimaita zabe a Kano: Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga, hotuna

Magoya bayan gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna damuwar su a kan zargin da suke yiwa rundunar ‘yan sanda na nuna kiyayya ga jam’iyyar APC yayin zaben gwamna da aka yi a jihar ran Asabar, 9 ga watan Maris.

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewar dandazon matasan sun taru a fadar sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, daga inda su ka dunguma zuwa gidan gwamnatin jihar Kano domin kai kukan su.

Matasan sun bukaci rundunar ‘yan sanda ta tsaya ga aikinta na tabbatar da tsaro a zaben gwamnan jihar da za a maimaita a wasu mazabu a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Kazalika sun bukaci a bar hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da zabe ba tare da an yi kokarin tsoma baki a lamuran ta ba.

DUBA WANNAN: Ganduje: Dakta Baffa Bichi na APC ya ziyarci Abba Gida-gida har gida

Ganduje da jam’iyyar APC sun zargi kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Wakili, da nuna goyon baya ga Abba Kabir Yusuf, dan takarar jam’iyyar PDP, a zaben farko da aka gudanar ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Sai dai, Wakili, wanda sarki Sanusi II ya jinjinawa saboda jazircewar sa wajen yin aiki da gaskiya don tabbatar da tsaro, ya musanta zargin.

Maimaita zabe a Kano: Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga, hotuna
Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga
Asali: Facebook

Maimaita zabe a Kano: Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga, hotuna
masoya Ganduje sun yi zanga-zanga
Asali: Facebook

Maimaita zabe a Kano: Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga, hotuna
Masoya Ganduje sun yi zanga-zanga a Kano
Asali: Facebook

Maimaita zabe a Kano: Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga, hotuna
Dubban masoya Ganduje sun yi zanga-zanga
Asali: Facebook

Maimaita zabe a Kano: Dubun dubatar masoya Ganduje sun yi zanga-zanga, hotuna
Masoya Ganduje sun yi zanga-zanga
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel