Jama’a sun yi dafifi a lokacin da Ganduje ya kai ziyarar aiki mazabar Gama (Hotuna)

Jama’a sun yi dafifi a lokacin da Ganduje ya kai ziyarar aiki mazabar Gama (Hotuna)

Al’umma mazauna mazabar Gama sun yi fitar farin dango don tarbar gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayin daya kai ziyarar aiki zuwa mazabar da nufin gane ma idanunsa matsayin aikin sabon titin da aka fara a makon data gabata.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 18 ga watan Maris ne Gwamna Ganduje ya kai wannan ziyarar aiki, amma isarsa keda wuya sai ga daruruwan mutane sun mamayeshi, suna yi masa fatan alheri, tare da addu’ar samun nasararsa a zaben gwamnan jahar dake karatowa.

Jama’a sun yi dafifi a lokacin da Ganduje ya kai ziyarar aiki mazabar Gama (Hotuna)
Ganduje a Gama
Asali: UGC

KU KARANTA: Hamid Ali ya karrama jami’in kwastam da yayi watsi da tayin cin hancin N152m

Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da shugaban jam’iyyar APC reshen jahar Kano, Abdullahi Abbas dan Sarki, da kuma sauran manyan masu rike da mukaman gwamnati, da kuma fitattun yan siyasa daga Gama.

Jama’a sun yi dafifi a lokacin da Ganduje ya kai ziyarar aiki mazabar Gama (Hotuna)
Ganduje a Gama
Asali: UGC

Sauran ayyukan da gwamnatin jahar Kano take gudanarwa a yanzu sun hada da kwashe bola, da kuma gina sabbin famfon tuka tuka guda goma sha daya a layuka daban daban na unguwar Gama da kewayenta.

Mazabar Gama na cikin karamar hukumar Nassarawa ne, kuma tana daga cikin mazabun da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, zata sake gudanar da zaben maimaici a cikinsu don samar da sahihin sakamakon zaben gwamnan jahar a ranar 23 ga watan Maris.

Jama’a sun yi dafifi a lokacin da Ganduje ya kai ziyarar aiki mazabar Gama (Hotuna)
Ganduje a Gama
Asali: UGC

Baya da Gama, akwai mazabu 210 da da hukumar INEC zata sake gudanar da zaben gwamnan a cikin kananan hukumomi 22, sakamakon kuri’un da suka lalace a zaben daya gabata guda 128,572 sun haura bambamcin kuri’un dake tsakanin Ganduje da Abba gida gida, 16,655.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel