Da duminsa: Shugaban kasar Khazak ya yi murabus bayan shafe shekaru 29 yana mulki

Da duminsa: Shugaban kasar Khazak ya yi murabus bayan shafe shekaru 29 yana mulki

Shugaban kasar Kazakhstan, Nursultan Nazarbayev ya sanar da murabus dinsa daga shugabantar kasar a ranar Talata, bayan shafe shekaru 29 a kan mulkin kasar, lamarin da ya girgiza da yawan al'ummar kasar musamman ma mukarrabansa da ke gwamnatin.

"Na yanke shawarar yin murabus daga kujerar shugaban wannan kasa," a cewarsa, yayin gabatar da wani jawabin kai tsaye a gidan talabijin mallakin kasar.

Nazarbayev ya hau mulkin kasar wacce ke cike da arzikin man fetur tun a lokacin da ta ke karkashin mulkin gurguzu, kuma bai taba nuna wani mahaluki a matsayin wanda ya ke so ya gaje shi ba.

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'in INEC a jihar Jigawa

Da duminsa: Shugaban kasar Khazak ya yi murabus bayan shafe shekaru 29 yana mulki
Da duminsa: Shugaban kasar Khazak ya yi murabus bayan shafe shekaru 29 yana mulki
Asali: Twitter

Wannan matakin na sa ya zo ne a dai dai lokacin da tattalin arzikin kasar ke kan farfadowa bayan durkushewar farashin man fetur a shekarar 2014, da kuma rashin ababen more rayuwa da suka yiwa kasar katutu.

Nazarbayev zai samu garabas manyan mukamai na iyayen kasa masu fada aji biyo bayan wannan murabus nasa, godiya ga matsayinsa a kasar na zama "shugaban mulkin nahiyar." Haka zalika, a shekarar da ta gabata ne ya zamo shugaban majalisar tsaro ta kasar mafi dadewa.

A shekarar 2015, Nazarbayev ya lashe zaben kasar da kusan kuri'u 98 na kuri'un da aka kada gaba daya, wanda kuma har ake sa ran zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a 2020.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel