Sonni Ogbuoji ya sa APC ta fadi zabe a Jihar Ebonyi – Ogbonnoya Onu

Sonni Ogbuoji ya sa APC ta fadi zabe a Jihar Ebonyi – Ogbonnoya Onu

- Wadanda su ka nemi Gwamna a APC a Ebonyi sun zargi 'Dan takaran su da laifuffuka

- ‘Ya ‘yan Jam’iyyar sun ce Sonni Ogbuoji yana yi masu kulalliya a Jihar Ebonyi a boye

- Ana kuma zargin Ogbuoji da tattara kudin yakin neman zaben Jam’iyyar APC a Jihar

Sonni Ogbuoji ya sa APC ta fadi zabe a Jihar Ebonyi – Ogbonnoya Onu
Ana zargin Sanata Sonni Ogbuoji da yi wa APC zagon kasa
Asali: Twitter

Wasu daga cikin wadanda su kayi takarar kujerar gwamnan jihar Ebonyi a karkashin jam’iyyar APC mai adawa a jihar sun hurowa ‘dan takaran su, Sonni Ogbuoji, wuta da cewa ya yaudari jam’iyyar a zaben da aka yi kwanaki.

Kamar yadda mu ka ji, wadannan ‘ya ‘yan APC sun fadawa Duniya cewa Sanata Sonni Ogbuoji ya yi wa jam’iyyar APC zagon kasa inda ya hada-kai wajen kifar da jam’iyyar da kasa, ya kuma sace kudin kamfe da aka tara a zaben.

Ogbonnaya Onu, wani ‘dan takarar majalisar tarayya na APC a jihar, shi ne yayi magana a madadin sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar. Onu yayi kira ga shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole da ya binciki abin da ya faru a jihar.

KU KARANTA: Rikicin APC ta sa an maka Jam’iyya gaban babban Kotun Najeriya

Onu yace Sanata Ogbuoji shi ne ya jawowa APC shan kasa a zaben da aka yi inda ya lamushe kudin yakin neman zaben Jam’iyyar, sannan kuma ya ki maida hankali wajen ganin APC tayi abin da ya dace domin ta ci zaben 2019.

Haka kuma wadannan ‘yan APC su na zargin ‘dan takarar gwamnan da sauya sunayen wasu ‘yan takara na APC inda ya maye guraben su da ‘yan siyasar da ba su da farin jini. Onu yace sam ba yakin cin zabe Ogbuoji ya fito yi ba.

S. Ogbuoji ya karyata wannan zargi inda yace sharri ake masa. ‘Dan takarar gwamnan yayi wannan kawabi ne ta Darektan yada labarai na jirgin yakin neman zaben sa watau Ikenna Emewu. Emewu ya kalubalanci a kawo hujja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel