Majalisar wakilai ta dage zamanta zuwa 2 ga wata Afrilu

Majalisar wakilai ta dage zamanta zuwa 2 ga wata Afrilu

Majalisar wakilai ta dage zamanta zuwa ranar 2 ga watan Afrilu domin ba mambobinta damar zantawa da hukumomi a matakin kwamiti kan gabatar da tsarin kasafi kudin 2019.

Hakan ci gaba ne ga shawarar Shugaban masu rinjaye a majalisa, Femi Gbajabiamila (APC-Lagos) da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata, 19 ga watan Maris.

Da yake zantar da hukunci, mataimakin kakakin majalisa, Yussuf Lassun (APC-Osun), ya bukaci dukkanin kwamitocin majalisar da su yi aiki sannan su kammala muhawara kan kasafin kudin kafin watan Mayu.

Majalisar wakilai ta dage zamanta zuwa 2 ga wata Afrilu
Majalisar wakilai ta dage zamanta zuwa 2 ga wata Afrilu
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa dokar kasafin kudi ya kammalu don gabatar da shi da zaran sun dawo majaisa a atan Mayu.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince da mafi karancin albashin ma'aikata N30,000 da fadar shugaban kasa ta gabatar kafin zaben shugaban kasa a watan Febrairu, 2019.

KU KARANTA KUMA: Kano: Na riga na kafa majalisar Abba gida-gida - Kwankwaso

Kwamiti na musamman da majalisar ta nada karkashin jagorancin Sanata Francis Alimekhena, ta gabatar da rahotonta da safiyar Talata, 19 ga wtaan Maris, 2018. Majalisar ta bukaci fadar shugaban kasa da ta aiko karin kasafin kudi domin iya biyan wannan sabon kudin ma'aikata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel