Da zafinsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'in INEC a jihar Jigawa

Da zafinsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'in INEC a jihar Jigawa

- Rahotanni na nuni da cewa wasu 'yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani jami'in hukumar INEC, Mr Mahadi Hassan, a jihar Jigawa

- Rundunar 'yan sandan ta ce har yanzu babu wani korafi da hukumar zaben ko iyalan wanda aka yi garkuwan da shi suka shigarwa rundunar

- Sai dai kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mr Bala Zama, ya shaidawa manema labarai cewa 'yan bindigar sun tuntubi iyalan jami'in hukumar zaben kan batun kudin fansa

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani jami'in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Mr Mahadi Hassan, a jihar Jigawa.

Shugaban sashen ilimanar da wasu kad'a kuri'a da kuma hulda da jama'a na hukumar INEC na jihar Jigawa, Mr John Kaiwa ya tabbatar da hakan ga Channels Tv a ranar Talata.

Ya bayyana cewa an yi garkuwa da Hassan ne tun a ranar Juma'a a kan titin zuwa Gwiwa da ke jihar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: INEC ta bi umurnin kotu, ta daina karbar sakamakon zaben Bauchi

Da zafinsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'in INEC a jihar Jigawa
Da zafinsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'in INEC a jihar Jigawa
Asali: Facebook

Haka zalika ita ma rundunar 'yan sanda ta jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin.

Rundunar 'yan sandan ta ce har yanzu babu wani korafi da hukumar zaben ko iyalan wanda aka yi garkuwan da shi suka shigarwa rundunar.

Sai dai kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mr Bala Zama, ya tuntubi kwamishinan INEC na jihar, Dr Mahmooud Isah, inda ya shaidawa manema labarai a Dutse cewa 'yan bindigar sun tuntubi iyalan jami'in hukumar zaben kan batun kudin fansa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel