Da duminsa: INEC ta bi umurnin kotu, ta daina karbar sakamakon zaben Bauchi

Da duminsa: INEC ta bi umurnin kotu, ta daina karbar sakamakon zaben Bauchi

Rahotan da Legit.ng Hausa ta samu yanzu yanzu na nuni da cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da ci gaba da karbar sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi, wanda ta fara karba a ranar Talata, 19 ga watan Maris, 2019.

Kamar yadda Channels TV ta wallafa, hukumar ta yanke wannan hukunci ne bayan da wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar zaben da ta tsayar da karbar zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar ta Bauchi.

A baya bayan nan, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa; Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC daga ci gaba da karbar sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi wanda ya gudana a ranar 9 ga watan Maris.

KARANTA WANNAN: Mutu ka raba: Har gobe ina tare da Atiku, ba zan juya masa baya ba - Gbenga Daniel

Da duminsa: INEC ta bi umurnin kotu, ta daina karbar sakamakon zaben Bauchi
Da duminsa: INEC ta bi umurnin kotu, ta daina karbar sakamakon zaben Bauchi
Asali: Twitter

Hukuncin wanda kotun ta bayar ya zo ne bayan da gwamnan jihar Bauchi mai ci a yanzu, Mohammed Abubakar da jam'iyyar APC suka shigar da kara, wanda kuma hukuncin zai ci gaba har sai an war ware shari'ar tsakanin bangarorin biyu.

A cikin takardar korafin, APC da Abubakar sun roki kotun da ta bayar da umurni da zai hana hukumar INEC dawowa da karbar sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa wanda jhukumar ta soke a baya dangane da zaben kujerar gwamnan jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel