Mutu ka raba: Har gobe ina tare da Atiku, ba zan juya masa baya ba - Gbenga Daniel

Mutu ka raba: Har gobe ina tare da Atiku, ba zan juya masa baya ba - Gbenga Daniel

- Gbenga Daniel, tshohon gwamnan Ogun, ya ce har yanzu yana tare da Atiku Abubakar kuma ba zai iya rabuwa da shi ba

- A baya bayan nan Mr Daniel ya sanar da matakinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP da kuma yin ritaya daga siyasa gaba daya

- Sai dai har yanzu Atiku ko shuwagabannin jam'iyyar PDP ba su ce 'uffan' akan wannan murabus na Mr Daniel daga jam'iyyar ko harkokin siyasa ba

Gbenga Daniel, tshohon gwamnan Ogun, ya ce har yanzu yana tare da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, kuma ba zai iya rabuwa da shi ba.

Mr Daniel wanda ya taba kasancewa babban daraktan yakin zaben Atiku Abubakar, a baya bayan nan ya sanar da matakinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP da kuma yin ritaya daga siyasa gaba daya.

Sai dai wannan mataki na Mr Daniel bai yiwa mambobin jam'iyyar PDP dadi ba, inda har wasu suka fara zargin cewa yana yunkurin sauya sheka ne zuwa APC, ganin yadda yayi aiki kafada-da-kafada da dan takarar gwamnan jihar Ogun karkashin jam'iyyar APC a zaben gwamnoni a aka kammala.

KARANTA WANNAN: Ana wata ga wata: Jam'iyyar PDM ta garzaya kotu akan sakamakon zaben Bauchi

Mutu ka raba: Har gobe ina tare da Atiku, ba zan juya masa baya ba - Gbenga Daniel
Mutu ka raba: Har gobe ina tare da Atiku, ba zan juya masa baya ba - Gbenga Daniel
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, OGD kamar yadda yafi kiran kansa da sunan, ya ce ya yi murabus daga PDP kuma ya yi murabus daga siyasa gaba daya, bayan shafe kusan shekaru 20 yana a cikin harkokin siyasa.

Sai dai har yanzu Atiku ko shuwagabannin jam'iyyar PDP ba su ce 'uffan' akan wannan murabus na Mr Daniel daga jam'iyyar ko harkokin siyasa ba.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa tsohon shugaban kasa Gooduck Jonathan, ya jagoranci wata tawagar jagororin jam'iyyar PDP, inda suka gana da Mr Daniel domin tausasa zuciyarsa akan sauya wannan mataki da ya dauka.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel