Ana wata ga wata: Jam'iyyar PDM ta garzaya kotu akan sakamakon zaben Bauchi

Ana wata ga wata: Jam'iyyar PDM ta garzaya kotu akan sakamakon zaben Bauchi

- Jam'iyyar PDM, ta ce ba ta amince da sakamakon zaben gwamnan jihar da na 'yan majalisun dokoki ba

- PDM ta yi ikirarin cewa INEC ta cire tambarin jam'iyyarta a jikin takardun dangwala kuri'a a lokacin ranar Asabar, 19 ga watan Maris

- Jam'iyyar na kallon cire tambarinta da INEC ta yi a matsayin "rashin adalci tsantsa" da kuma "tauye hakkin bil Adama na ka zaba a zabeka."

Jam'iyyar PDM, ta ce ba ta amince da sakamakon zaben gwamnan jihar da na 'yan majalisun dokoki ba, sakamakon cire tambarin jam'iyyarta a jikin takardun dangwala kuri'a a lokacin zaben gwamnonin da ya gudana a ranar Asabar, 19 ga watan Maris.

Jam'iyyar a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a yammacin ranar Litinin, dauke da sa hannun sakatarenta na jihar, Alhaji Sani M. Waziri, ta bayyana cewa shuwagabanni da mambobin jam'iyyar na kallon cire tambarinta da INEC ta yi a matsayin "rashin adalci tsantsa" da kuma "tauye hakkin bil Adama na ka zaba a zabeka.".

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: Mun haramtawa INEC karbar sakamakon zaben Bauchi - Kotu

Aana wata ga wata: Jam'iyyar PDM ta garzaya kotu akan sakamakon zaben Bauchi
Aana wata ga wata: Jam'iyyar PDM ta garzaya kotu akan sakamakon zaben Bauchi
Asali: UGC

PDM ta yi ikirarin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta cire tambarinta daga jikin takardun kad'a kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.

Ta kara da cewa har ila yau INEC ba ta sanya tambarin jam'iyyar ba a jikin takardun zaben gwamna da na 'yan majalisun tarayya.

Jam'iyyar ta ce cire tambarinta ya sabawa dokar zabe ta 2010 (kamar yadda aka sabunta), inda PDM ta yi nuni da cewa ba za ta amince da sakamakon gwamna da na 'yan majalisun dokokin jihar Bauchi ba kuma za ta kai kara kotun zabe domin a kwatar mata hakkinta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel