Yanzu Yanzu: Motar makaranta dauke da yara sama da 40 yayi hatsari a Ekiti

Yanzu Yanzu: Motar makaranta dauke da yara sama da 40 yayi hatsari a Ekiti

Wata babbar motar bus dauke da yaran makarantar St Lawrence sama da 40 yayi hatsari a afiyar yau Talata, 19 ga watan Maris a hanyar Textile da ke Ado-Ekiti.

Motar ya kwace ne daga hannun direban sannan ya shilla ta kan titi zuwa dayan bangaren hanyar.

Babu rahoton wadanda suka mutu a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A wani lamari makamanin haka, Legit.ng ta rahoto cewa wani abun bakin ciki ya faru a karamar hukumar Dange Shuni da ke jihar Sokoto a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, inda wata matashiya yar ajin karshe a jami’a mai suna Munirah Adamu ta rasa ranta da misalin karfe 4:30pm a wani mumunan hatsari a hanyarta na dawowa daga makaranta a jihar Zamfara.

An wallafa labarin mumunan lamarin ne a nshafin Twitter na wani mai suna @Ibrahim_Bello inda ya wallafa labarin tare da katin shaidar marigayar.

Afkuwar hatsarurruka na daga cikin manyan kalubalen da gwamnatin Najeriya ke fuskanta. Yan makonni da suka gabata iyalan wata matashiyar yarinya mai suna Kemi Adeniran sun shiga halin bakin ciki biyo bayan mutuwarta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na ganawar sirri da shugabannin tsaro a fadar Shugaban kasa

Kemi Adeniran, wacce ta kamala karatu daga jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko (AAUA) ma ta gamu da ajalinta ne a wani hatsari da ya afku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel