Lalong ya bayyana dalilin da yasa ya kaiwa Buhari ziyara

Lalong ya bayyana dalilin da yasa ya kaiwa Buhari ziyara

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya ce ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari ne a fadarsa da ke Abuja domin su tattauna game da tsarin tsaro da za a samar domin sauran zabukan da za a gudanar a jihar.

A ziyarar da Lalong ya kaiwa shugaban kasar a ranar Litinin, ya ce sun kuma tattauna a kan kallubalen satar shanu da ya yiwa jihar katutu.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta tsayar da ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zabukan da ba a kammala ba a jihohin Adamawa, Kano, Sokoto, Benue, da Filato.

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

Gwamna Lalong ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Buhari
Gwamna Lalong ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Buhari
Asali: Twitter

A yayin da ya ke hira da manema labarai, Lalong ya ce: "Kawo yanzu, mun gudanar da zabe cikin zaman lafiya. Za mu dawo domin karasa zabukan a wuraren da ba a kammala ba. Ina son INEC ta gudanar da zabe cikin zaman lafiya saboda haka muna son jami'an tsaro su kasance suna cikin shiri. Wannan shine abinda na tattauna da shugban kasa."

Da aka masa tambaya ko yana fargaba duba da cewa zaben ya matso kusa, ya ce: "Don mene zanyi fargaba tunda dukkan kuri'un da aka soke nawa ne? Wuraren da na lashe zabe aka soke. Babu wata bukatar soke kuri'u amma a matsayi na na lauya ina son inyi biyaya ga doka. Bana son in fara magana a kan tauye hakki tunda sakamakon zaben ya bayyana."

A yayin da ya ke magana a kan satar shanu da akayi a jihar a ranar Alhamis da ta gabata inda aka sace shanu fiye da 100 a kusa da Kwallejin aikin Akanta na Kwall da ke karamar hukumar Bassa na jihar, ya kara da cewa: "Wannan shine dalilin da yasa na ke damuwa a kan samar da tsaro, dama kamar haka ake farawa daga satan shanu sai kaji an fara rikici tsakanin manoma da makiyaya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel