Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta amince da mafi karancin albashin N30,000

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta amince da mafi karancin albashin N30,000

Labarin dake shiga mana da duminsa na nuna cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince da mafi karancin albashin ma'aikata N30,000 da fadar shugaban kasa ta gabatar kafin zaben shugaban kasa a watan Febrairu, 2019.

Kwamiti na musamman da majalisar ta nada karkashin jagorancin Sanata Francis Alimekhena, ta gabatar da rahotonta da safiyar Talata, 19 ga wtaan Maris, 2018.

Majalisar ta bukaci fadar shugaban kasa da ta aiko karin kasafin kudi domin iya biyan wannan sabon kudin ma'aikata.

KU KARANTA: Rochas Okorocha ya mutu murus a siyasa - Jigo a APC

A baya mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya wato NLC karkashin jagorancin shugaban kungiyar ta kasa, Mista Ayuba Wabba, a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2019 a fadar shugaban kasa Aso Rock.

Kungiyar kwadagon ta kawowa shugaban kasan gaisuwar taya murna ne kan nasarar da ya samu a zaben ranar 23 ga watan Febraiuru, 2019 inda suka nuna farin cikinsu da yadda Buhari ke gudanar da al'umma.

A jawabin shugaban kungiyar Ayuba Wabba, ya yabawa shugaba Buhari musamman kan kudin fidda kai da ya taimakawa gwamnonin jihohi da shi domin biyan albashin ma'aikata da yan fansho.

A karshe yayi kira ga yan majalisar dokokin tarayya da su hanzarta wajen tafiyar da dokar karin kudin mafi karancin albashi da kuma shugaban kasa ya rattaba hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel