Sanatan Zamfara Marafa ya aikawa Kotun daukaka kara takarda

Sanatan Zamfara Marafa ya aikawa Kotun daukaka kara takarda

Mun ji labari Shugaban kwamitin harkar man fetur a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Marafa, ya rubuta takarda zuwa ga shugaban kotun daukakak kara ta Najeriya game da rigimar APC a jihar Zamfara.

Kabir Marafa ya aika takarda ne zuwa ga Alkali mai shari’a, Zainab Adamu Bulkachuwa, yana mai kokawa da bata lokacin da ake samu wajen nada mutanen da za su duba rikicin da ya barkowa jam’iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara.

Sanata Kabiru Marafa ya fadawa Mai shari’a Zainab Bulkachuwa cewa nawan da kotun ta take yi wajen fitar da kwamitin da za su saurari kukan ‘ya ‘yan APC a Zamfara, alamu ne da ke nuna za ayi masa rashin adalci a gaban shari’a.

KU KARANTA: Abin da ya sa Darektan yakin neman zaben Atiku ya bar PDP

Sanatan Zamfara Marafa ya aikawa Kotun daukaka kara takarda
Kabiru Marafa ya aikawa Mai shari'a Zainab Bulkachuwa takarda
Asali: Twitter

Marafa ya rubutawa shugabar kotun daukaka kara na kasar wannan takarda ne tun Ranar 13 ga Watan Maris. A wasikar Sanatan tare da wasu mutane 142 mai lamba CA/32/2019, ya nemi ayi gaggawa a duba karar da ya kawo gaban kotun.

Sanatan na Zamfara ta yamma ya tunawa kotu cewa akwai bukatar a duba lamarin APC na jihar cikin gaggawa kafin lokaci ya kure. Marafa yake cewa lokacin da doka ta tanada domin a dauki mataki a jam’iyya yana daf da kure masu.

Jam’iyyar APC wanda ke mulki a jihar Zamfara ta samu kan ta ne a cikin rikici wajen tsaida ‘dan takarar gwamna na zaben 2019. Wannan ya sa da farko aka haramtawa jam'iyyar APC shiga zaben jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel