Yanzu Yanzu: Buhari na ganawar sirri da shugabannin tsaro a fadar Shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Buhari na ganawar sirri da shugabannin tsaro a fadar Shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 19 ga watan Maris ya yi ganawar sirri tare da shugabannin tsaro. An fara ganawar ne a ofishin Shugaban kasa da ke fadar Shugaban kasa da misalin karfe 11 na safe.

Babu shakka tattaunawar zai kasance akan tabarbarewar tsaro a kasar da kuma yadda za a tabbatar da cikakken tsaro a jihohin da hukumar zabe mai zaman kanta za ta sake gudanar da zabe a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Har yanzu ana ci gaba da ganawar a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: EFCC na shirin bi ta kan gwamnoni masu barin gado

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Bbabban lauyan dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP. Livy Uzokwu, ya bayyana cewa lauyoyin jam'iyyar na da isassun hujjojin da zasu gabatar a gaban kotu domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Yayinda yake magana da manema labarai a Abuja, Lauyan ya ce duk da cewa sun samu matsala wajen duba kayayyakin da aka gudanar da zabe da su, ba zasuyi kasa a guiwa wajen shigar da kara ba.

Atiku ya bukaci kotun ta alantasa a matsayin wanda yayi nasara a zaben 23 Febrairu ko kuma a sake sabon laale.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel