Munada isassun hujjojin da zamu gabatar a kotu - Lauyan Atiku

Munada isassun hujjojin da zamu gabatar a kotu - Lauyan Atiku

Babban lauyan dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP. Livy Uzokwu, ya bayyana cewa lauyoyin jam'iyyar na da isassun hujjojin da zasu gabatar a gaban kotu domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Yayinda yake magana da manema labarai a Abuja, Lauyan ya ce duk da cewa sun samu matsala wajen duba kayayyakin da aka gudanar da zabe da su, ba zasuyi kasa a guiwa wajen shigar da kara ba.

Atiku ya bukaci kotun ta alantasa a matsayin wanda yayi nasara a zaben 23 Febrairu ko kuma a sake sabon laale.

KU KARANTA: Kisan Musulma a Nuzilan: Yadda na sha da kyar - Limamin Masallaci

Yace: "Inada imanin cewa munada isasshen hujjojin da zamu gabatar gaban kotu kuma ta amince mana. A shirye muke da kare kararmu saboda munada hujja. Mun shigar da kara kotu."

"Duk da cewan muna samu wasu kalubale wajen ganin kayayyakin zabe, mun shigar da kararmu cikin lokaci, za'a tilasta INEC tabi umurnin kotu domin bari mu ga kayayyakin zabe."

"Don mun shigar da kara ba yana nufin ba zamu iya amfani da kayayyakin ba idan muka same su daga INEC. Wasu mambobin kwamitin lauyoyin sun tafi wajen INEC sau uku a makon da ya gbaata amma ko yau (Litinin) a ce musu su dawo gobe (Talata)."

"Inada imanin cewa munada hujjojin kwato hakkinmu, kuma inada yaqinin cewa Alhaji Atiku Abubakar, ne ya lashe zaben."

A ranar Litinin, tawagar lauyoyin Atiku da jam'iyyar PDP sun shigar da kara kotu domin kalubalantar zaben shugaban kasar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel