- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar (EFCC) na shirin fara bincike a cikin ayyukan gwamnoni masu barin gado
- EFCC ta bayyana cewa ta dauki matakan da ya kamata domin tabbatar da cewa gwamnonin da abun ya shafa basu tsere daga kasar ba
- Hukumar tace hukunta gwamnonin masu barin gado zai fara da zaran sun mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu
Ana iya samun kura a sansanin gwamnoni masu barin gado a Najeriya yayinda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar (EFCC) ke shirin fara bincike a cikin ayyukansu.
Legit.ng ta fahimci cewa EFCC tace za ta fara hukunta gwamnoni masu barin gado, wadanda ke da zargin rashawa akan su.

Ana wata ga wata: EFCC na shirin bi ta kan gwamnoni masu barin gado
Source: Depositphotos
A bisa ga rahoton jaridar Daily Sun, EFCC tace hukunta gwamnonin masu barin gado zai fara da zaran sun mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Rahoton ya kara da cewa hukumar ta bayyana cewa ta dauki matakan da ya kamata domin tabbatar da cewa gwamnonin da abun ya shafa basu tsere daga kasar ba.
Hukumar dai ba ta ambaci sunayen gwamnonin da abun ya shafa ba.
KU KARANTA KUMA: Zaben Kano zai zama mizanin auna gaskiyar INEC – Kwankwaso
Sai dai gwamnoni wadanda za su bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu sun hada da Abdulfatah Ahmed (Kwara), Rochas Okorocha (Imo), Abiola Ajimobi (Oyo), Ibikunle Amosun (Ogun), Akinwunmi Ambode (Lagos), Kashim Shettima (Borno), Ibrahim Gaidam (Yobe) da kuma Ibrahim Dankwambo (Gombe).
Gwamnonin Sokoto, Adamawa , Bauchi, Plateau, Benue, Kano, Rivers basu san makomarsu ba har yanzu saboda an bayyana zabensu a matsayin ba kammalalle ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng