Kisan Musulma a Nuzilan: Yadda na sha da kyar - Limamin Masallaci (Hotuna)

Kisan Musulma a Nuzilan: Yadda na sha da kyar - Limamin Masallaci (Hotuna)

Daya daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a hari da aka kaiwa Masallatai biyu a kasar Nuzilan, wanda limami ne kuma dan asalin Najeriya, Lateef Alabi, ya bayyana yadda suka tsira daga mumunan hari.

Mutane 50 suka rasa rayukansu yayinda wani dan bindiga mai suna Brenton Tarrant ya kai hari masallatai biyu a birnin Christchurch ranar Juma'ar da ta gabata.

Lateef Alabi, wanda limami ne a masallacin Linwood, ya ce yana cikin Sallah ne yayinda ya fara jin karar harbin bindiga. Kawai sai ya katse Sallarsa domin ganin abinda ke faruwa.

Alabi ya fadawa jama'ar cikin masallacin sun kwanta akasa amma kafin ya farga, dan ta'addan ya hallaka masallata da dama.

KU KARANTA: Akwai abin tarihu guda daya da zan kafa a Najeriya – Buhari

Kisan Musulma a Nuzilan: Yadda na sha da kyar - Limamin Masallaci (Hotuna)
Kisan Musulma a Nuzilan: Yadda na sha da kyar - Limamin Masallaci (Hotuna)
Asali: Facebook

Yayinda harsashi ya kara masa, sai ya ajiye bindigan ya gudu. A lokacin ne wasu Musulmai suka kure masa gud kafin ya shiga motarsa ya gudu.

A cewar Limamin: "Ya harbi wani dan uwa a kai yayinda yake shigowa Masallacin. Sai na katse Sallah, na leka ta taga, sai naga wani mutumi da bindiga, sanye da kayan yaki. Duba waje na ke da wuya, sai naga gawawwaki a kasa, nace wannan dan ta'adda ne."

"Sai na fara kwashe gawawwakin domin sanin wadanda suka cika da masu rai. Ban taba tunanin hakan zai faru a Nuzilan ba."

Kisan Musulma a Nuzilan: Yadda na sha da kyar - Limamin Masallaci (Hotuna)
Limamin kenan a tsakiya
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel