Zaben Bauchi: Zan maka INEC a kotu kan maimaita zaben jihar - Gwamna Abubakar

Zaben Bauchi: Zan maka INEC a kotu kan maimaita zaben jihar - Gwamna Abubakar

Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar ya yi barazanar tafiya Kotu domin kalubalantar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), kan hukuncin da ta yanke na ci gaba da hada sakamakon zabe a Jihar.

Da farko hukumar zaben ta lissafta Bauchi a cikin Jihohin da za a gudanar da sabon zabe, amma daga baya kuma sai ta sauya shawara, inda ta ce za a ci gaba da kidayan sakamakon zaben da aka fara a ranar 9 ga watan Maris, a ranar Talata.

Da yake magana bayan ya gana da shugaba Buhari, a ranar Litinin, 18 ga watan Maris, gwamnan ya kwatanta shawarar ta INEC da cewa ba ta halasta ba.

Zaben Bauchi: Zan maka INEC a kotu kan maimaita zaben jihar - Gwamna Abubakar
Zaben Bauchi: Zan maka INEC a kotu kan maimaita zaben jihar - Gwamna Abubakar
Asali: Depositphotos

Da aka yi masa tambaya kan ko abin da ke faruwan daidai ne gwamnan na Bauci ya ce, “Tabbas, sam hakan ai bai halasta ba. wannan abu ne a fili.

“Ai babban jami’in zabe shi ne matuka ta karshe a kan abin da ya shafi shelanta sakamakon zabe. Kuma da zaran ya shelanta sakamakon zaben, ba wanda ya isa ya canza hakan, face kotun da doka ta yarda da ita.”

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya fara sake hada sakamakon zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa bayan ana tsaka da yaba mata da kuma sukarta.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kano zai zama mizanin auna gaskiyar INEC – Kwankwaso

Yayinda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi na’am da wannan mataki, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar ta soki lamarin.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Alhaji Hamza Koshe Akuyam, yayinda yake jawabi ga manema labarai, yace INEC ta dauki kyakyawan matakin da ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel