Atiku ya shigar da manyan korafi 5 domin kalubalantar sakamakon zabe

Atiku ya shigar da manyan korafi 5 domin kalubalantar sakamakon zabe

A yau Talata wasu daga cikin korafe-korafen da jam'iyyar PDP da kuma dan takarar ta na kujerar shugaban kasa yayin zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar, su ka shigar domin kalubalantar sakamakon zabe a jiya Litinin sun bayyana.

Atiku ya shigar da manyan korafi 5 domin kalubalantar sakamakon zabe
Atiku ya shigar da manyan korafi 5 domin kalubalantar sakamakon zabe
Asali: Twitter

Cikin takardar shigar da kara mai dauke da shafi 141, Atiku da jam'iyyar PDP sun shimfida wasu manyan korafe-korafe biyar ma su kalubalantar cancantar shugaban kasa Buhari ta jagorancin kasar nan da suka hadar da rashin samun mafi ƙanƙantar cancanta ta takardar kammala karatu da kundin tsarin mulki ya shar'anta.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta bayar da muhimmanci kan kiwon lafiya a bana - Ministan Kasafi

A yayin da manyan Lauyoyi 21 ke wakilcin Atiku da kuma jam'iyyar PDP a gaban Kuliya, akwai kuma kananan Lauyoyi 18 ma su kalubalantar sakamakon zabe gami da cancantar shugaban kasa Buhari ta jagorancin kasar nan.

Cikin jerin korafe-korafen da majiyar jaridar Legit.ng ta wassafa kamar yadda lauyoyin suka shimfida a gaban kotu sun hadar da cewa;

Shugaban kasa Buhari bai samu nasara ba ta hanyar adalci da gaskiya a yayin zaben kasa da aka gudanar.

Sake zaben Buhari na tattare da ribatar miyagun ababe na rashawa da kuma magudi da ba za su da iyaka

Nasarar Buhari a babban zabe na cin karo da shimfidar dokoki da kuma tanadi na shari'a kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta gindaya.

Shugaban kasa Buhari ba ya da cancantar tsayawa takara tun gabanin zaben kasa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Cewa shugaban kasa Buhari na amfani da takardun shaidar kammala karatu na bogi wajen jagorantar al'ummar kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel