Gwamnatin tarayya za ta bayar da muhimmanci kan kiwon lafiya a bana - Ministan Kasafi

Gwamnatin tarayya za ta bayar da muhimmanci kan kiwon lafiya a bana - Ministan Kasafi

Gwamnatin tarayya da sanadin Ministan Kasafi da tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma, ta bayyana sashen gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bai wa mafificin muhimmanci a shekarar nan ta 2019.

Ministan Kasafi da tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma, ya bayyana cewa duk da hawa da sauka na samun kudaden shiga a kasar nan, shugaban kasa Buhari zai bayar da mafificin muhimmanci wajen fitar da dukiya domin inganta harkokin kiwon lafiya a kasar nan.

Ministan Kasafi da tsare-tsaren kasa; Udoma Udo Udoma
Ministan Kasafi da tsare-tsaren kasa; Udoma Udo Udoma
Asali: Twitter

Udoma ya bayar da shaidar hakan a yau Talata yayin wani taron kara wa juna sani akan muhimmancin sanya hannun jari a bangaren kiwon lafiya da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Ministan ya bayyana yadda gwamnatin shugaban kasa Buhari ke ci gaba da jajircewa wajen saukaka yawaitar mace-macen rayuka a Najeriya da a halin yanzu ta kasance cikin sahun gaba a nahiyyar Afirka.

Ya kuma yi kira ga dukkanin bangarori da masu ruwa a tsaki cikin harkokin gwamnati da su jajirce wajen habaka hanyoyin samar da kudaden shiga domin inganta sashen kiwon lafiya da ta kasance jari ga dukkanin mai numfashi a doron kasa.

KARANTA KUMA: Tsaffin Jakadu sun nemi a soke maimacin zaben gwamnan jihar Benuwe

Cikin wani rahoton da shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito ta bayyana cewa, a yau cikin fadar sa ta Villa shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin tawagar gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, inda daga bisani ya shiga bayan Labule tare da shugabannin tsaro na kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel