Boko Haram: Bayan kai hari, tarzoma ta lafa a garin Michika

Boko Haram: Bayan kai hari, tarzoma ta lafa a garin Michika

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, kungiyar ma su tayar da kayar baya ta Boko Haram sun kutsa cikin garin Michika da ke jihar Adamawa a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, daruruwan mazauna yankin sun bayyana yadda kutsen maharan rike da Makamai na kare dangi ya sanya suka arce cikin dokar daji domin neman mafaka da kuma tsira.

Boko Haram: Bayan kai hai, tarzoma ta lafa a garin Michika
Boko Haram: Bayan kai hai, tarzoma ta lafa a garin Michika
Asali: Depositphotos

Sai dai mun samu cewa, mayakan Boko Haram ba su samu cimma wata babbar nasara ba inda tuni tarzoma ta lafa a garin Michika yayin da rundunar dakarun soji ta yi gaggawar tunkarar wannan mummunan lamari da ya auku cikin duhun dare.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, makarantu da wuraren kasuwanci sun ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum kamar yadda wani mazaunin garin Michika, Abdulrahman Mutawalle ya bayyana.

KARANTA KUMA: Shari'ar Onnoghen: Gwamnatin tarayya ta shigar da korafi gabanin a kammala bincike - Akpala

A yayin da rayukan mutane akalla biyar sun salwanta tare da jikkatar da dama gami da asarar dukiya yayin aukuwar wannan mummunan hari, kwamishinan yada labarai da tsare-tsare na jihar, Mallam Ahmad Sajoh, ya bayyana cewa, gwamnati na ci gaba da kimanta girman ta'adi da harin ya haifar.

Mallam Sajoh ya kara da cewa, ba ya ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya, wadanda suka raunata a sakamakon tartsatsi na harsashin bindiga na ci gaba da samun kulawa a manyan asibitin garin Michika, Yola da kuma Mubi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel