Shari'ar Onnoghen: Gwamnatin tarayya ta shigar da korafi gabanin a kammala bincike - Akpala

Shari'ar Onnoghen: Gwamnatin tarayya ta shigar da korafi gabanin a kammala bincike - Akpala

Mista James Akpala, daya daga cikin jiga-jigan Lauyoyi ma su shaidar alkalin alkalai na Najeriya da aka dakatar, Walter Onnoghen, ya bayyana wani babban kuskure da gwamnatin tarayya ta yi gabanin shigar da korafin ta a gaban Kuliya.

A jiya Litinin, Mista James Akpala, daya daga cikin manyan lauyoyi masu gudanar da bincike a cibiyar tabbatar da da'a ta CCB, Code of Conduct Bureau, ya yi na'am da cewar gwamnatin tarayya ta yi kuskuren gabanin shigar da karar alkalin alkalai da aka dakatar, Walter Onnoghen.

Justice Walter Onnoghen
Justice Walter Onnoghen
Asali: UGC

Mista Akpala ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta yi kuskuren da ya sabawa doka da kuma shari'a yayin da ta shigar da karar alkalin alkalai gabanin Lauyoyi su kammala bincike akan zargin da ake ma sa na rashin bayyana dukkanin dukiyar da ya mallaka.

Babban Lauya Akpala na daya daga cikin jiga-jigan Lauyoyi ma su gabatar da shaida wajen karar Mista Onnoghen a gaban kotun tabbatar da da'a ta CCT, inda ake tuhumar sa da laifuka shidda da su ka sabawa dokokin kasa.

Ba ya ga laifin rashin bayyana dukkanin dukiya da kuma kadarori da ya mallaka, gwamnatin tarayya cikin korafin ta mai lamba CCT/ABJ/01/19, na tuhumar Mista Onnoghen da laifin mallakar asusu biya na ajiyar kudaden kasashen ketare da ya sabawa sashe na 15 sakin layi na 2 cikin dokokin kotun tabbatar da da'a ta CCT, Code of Conduct Tribunal.

KARANTA KUMA: Zababbun Sanatoci: Shekarau ya ciri tuta ta samun yawan adadin kuri'u a zaben bana

Sai dai gwamnatin tarayya bisa ga madogara ta shaida ta bayyana cewa, ta yanke hukuncin shigar da karar Mista Onnoghen a sanadiyar shawarar cibiyar CCT inda a halin yanzu alkali mai shari'a, Danladi Umar ke ci gaba da jagorantar zaman kotun.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel