Zababbun Sanatoci: Shekarau ya ciri tuta ta samun yawan adadin kuri'u a zaben bana

Zababbun Sanatoci: Shekarau ya ciri tuta ta samun yawan adadin kuri'u a zaben bana

Biyo bayan babban zabe na shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da aka gidanar a ranar 23 ga watan Fabrairu, binciken manema labarai na jaridar Daily Trust ya bankado yadda wasu zababbun Sanatoci su ka ciri tuta ta fuskar yawan kuri'u da aka kada ma su yayin zabe.

Binciken jaridar ya tabbatar da cewa, tsohon gwamnan jihar Kano kuma sabon zababben Sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau, ya yiwa sauran ‘yan majalisar tarayya fintinkau ta fuskar samun yawan kuri'u da magoya baya suka kada ma sa yayin zabe.

Kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta fidda sakamakon zabe, Mallam Shekarau wanda ya yi takara a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, ya yi nasara da zunzurutun kuri'u 506,271 a mazabar shiyyar Kano ta Tsakiya.

Mallam Ibrahim Shekarau
Mallam Ibrahim Shekarau
Asali: Depositphotos

Babban abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Aliyu Madakin Gini, ya rashin sa'a duk da samun kuri'u 267,778, kasa da ‘yan dubunnan kuri'u 273,404 da zababben gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha ya samu.

Shiyyar Kano ta Tsakiya ta kunshi kananan hukumomi 15 da suka hadar da; Dala, Gwale, Dawakin Kudu, Gezawa, Fagge, Garun Malam, Kano Municipal, Kumbotso, Kura, Madobi, Nasarawa, Minjibir, Ungogo, Warawa da kuma Tarauni.

Kazalika tsohon gwamnan Kano kuma Sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya Rabi'u Kwankwaso, ya kasance zababben Sanata mafi samun yawan adadin kuri'u kimanin 758,383 yayin zaben 2015 da ya gabata.

KARANTA KUMA: Atiku ya tanadi fiye da shaidu 400 domin kalubalantar sakamakon zabe

A yayin da zababben Sanatan shiyyar Katsina ta Kudu na jam'iyyar APC, Bello Mandiya ya ke take bayan Shekarau da kuri'u 433,139, Kabir Barkiya na jam’iyyar APC da ya samu kuri'u 340,800 a shiyyar Katsina ta Tsakiya, ya kasance a mataki na uku cikin jerin zababbun Sanatoci da suka yi zarra ta yawan samun kuri'u a zaben bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel