Da dumin sa: Hamid Ali yayi wani muhimmin nadi a hukumar Kwastam

Da dumin sa: Hamid Ali yayi wani muhimmin nadi a hukumar Kwastam

Shugaban hukumar hana fasa-kwauri ta kasa watau Kwastam, Kanal Hameed Ibrahim Ali mai ritaya ya nada Kwanturola Bashir Abubakar a matsayin mataimakin kwanturola na kasa kuma Sakataren majalisar zartaswar hukumar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na hukumar, DC Joseph Attah ya fitar da safiyar ranar Talata.

Da dumin sa: Hamid Ali yayi wani muhimmin nadi a hukumar Kwastam
Da dumin sa: Hamid Ali yayi wani muhimmin nadi a hukumar Kwastam
Asali: Facebook

KU KARANTA: Najeriya na kashe $5,000,000 wajen shigo da man ja

Sanarwar ta bayyana cewa tuni har shi wanda aka nada sabon mukamin, ya mika ragamar kujerar sa ta da zuwa ga mai bi masa Kwanturola Abba Kura.

A wani labarin kuma, Mista Godwin Emefiele, shugaban babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya bayyana cewa 'yan Najeriya na kashe kudaden da suka kai akalla Dalar Amurka miliyan dari biyar a duk shekara wajen shigo da man ja daga kasashen waje.

Shugaban Central Bank of Nigeria (CBN) din yayi wannan ikirarin ranar Litinin din da ta gabata da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na masu sana'ar man ja a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Taron dai kamar yadda muka samu ya samu halartar gwamnonin jahohin Akwa Ibom, Edo da Abiya. Haka ma shugabanni daga kamfanonin 'yan kasuwa kamar su Dangote, Flour Mills, United Food Industries da ma Dufil Prima Foods Plc dukkan su sun halarci taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel