Zaben Kano zai zama mizanin auna gaskiyar INEC – Kwankwaso

Zaben Kano zai zama mizanin auna gaskiyar INEC – Kwankwaso

- Dr Rabiu Kwankwaso ya ce zaben gwamna da za a sake gudanarwa a jihar Kano zai tabbatar ko kuma rushe darajar gwamnati da hukumar zabe mai zaman kanta

- INEC ta sanya ranar Asabar, 23 ga watan Maris a matsayin ranar sake zabe a Kano da wasu jihohi

- Zaben Kano dai na ci gaba da jan hankulan jama'a harma a kasashen ketare

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya jadadda cewa zaben gwamna da za a sake gudanarwa a jihar zai tabbatar da darajar gwamnati da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ko kuma ya nuna akasin haka.

Zaben Kano zai zama mizanin auna gaskiyar INEC – Kwankwaso
Zaben Kano zai zama mizanin auna gaskiyar INEC – Kwankwaso
Asali: UGC

Jihar Kano ta kasance daya daga cikin jihohi biyar da INEC ta kaddamar da cewar za ta sake gudanar da zabe a cikinsu, a ranar 23 ga watan Maris.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar zaben ta ce zaben jihar ba ta kammalu ba sanadiyar soke sakamakon wasu mazabu, wadanda yawan kuri'unsu suka haura yawan tazarar da ke tsakanin manyan 'yan takara biyu na PDP da APC a zaben na gwamna da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

A wani lamari na daban, mun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya fara sake hada sakamakon zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa bayan ana tsaka da yaba mata da kuma sukarta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Duk wanda ya ci zaben Gwamna a Kano, a ba shi kurum a huta – Sheikh Kabara

Yayinda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi na’am da wannan mataki, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar ta soki lamarin.

Hedkwatar INEC wanda ke da zama a hanyar Ahmadu Bello Way da ke garin Bauchi na cike da tsaro a tun bayan zaben gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel