Zabe: An tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC na Bauchi

Zabe: An tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC na Bauchi

- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya fara sake hada sakamakon zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa

- Yayinda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi na’am da wannan mataki, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar ta soki lamarin

- Hedkwatar INEC wanda ke da zama a hanyar Ahmadu Bello Way da ke garin Bauchi na cike da tsaro a tun bayan zaben gwamna

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya fara sake hada sakamakon zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa bayan ana tsaka da yaba mata da kuma sukarta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yayinda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi na’am da wannan mataki, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar ta soki lamarin.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Alhaji Hamza Koshe Akuyam, yayinda yake jawabi ga manema labarai, yace INEC ta dauki kyakyawan matakin da ya kamata.

Zabe: An tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC na Bauchi
Zabe: An tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC na Bauchi
Asali: UGC

Sai dai a nata bangaren APC, a wani jawabi daga shugabanta, Alhaji Uba Ahmed Nana, yace hukuncin da INEC ta yanke ya sama dokar zaben na 2010 da kuma tsarin gudanarwar zaben 2019.

Hedkwatar INEC wanda ke da zama a hanyar Ahmadu Bello Way da ke garin Bauchi na cike da tsaro a tun bayan zaben gwamna.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na kashe Dala miliyan 500 wajen shigo da man ja duk shekara - CBN

An toshe zirga-zirga a hanya yayinda motocin yan sanda da sojoji suka rufe hanya daya.

Tun bayan bayyana zaben jihar a mat6sayin ba kammalalle ba yanayin jihar ya shiga zullumi yayinda APC da PDP da magoya bayansu ke zargin junansu da shirya hakan don yin magudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel