Tattalin arziki: Amurka ta karbe kasuwar fetur din Najeriya a Indiya

Tattalin arziki: Amurka ta karbe kasuwar fetur din Najeriya a Indiya

A halin yanzu da aka shiga wata yarjejeniya tsakanin kasar Indiya da kuma Amurka, inda Indiya za ta rika sayen man fetur daga hannun Amurka, mun ji cewa Najeriya ta shiga matsala a kasuwan Duniya.

Kasar Indiya za ta shigo da gangar mai 600, 000 daga Amurka wanda hakan zai zama barazana ga Najeriya wanda a baya ita ce ta fi kowace kasa saidawa Indiya man fetur. Hakan dai na iya kawowa tattalin arzikin Najeriya cikas.

A cikin shekaru 5 zuwa 6 da suka wuce Indiya tayi wa Najeriya gagarumin ciniki na gangunan man fetur wanda da shi Najeriya ta ke samun kusan duk kudin shigan ta. Da alamu nan gaba kadan Amurka za ta girgiza kasuwar Najeriya.

KU KARANTA: Bincike ya nuna cewa Maza sun kusa karewa a duniya

Tattalin arziki: Amurka ta karbe kasuwar fetur din Najeriya a Indiya
Man fetur din Najeriya yana rage kasuwa a kasar waje
Asali: Facebook

Reuters ta rahoto cewa fiye da jiragen ruwa 30 da ke dauke da kayan man fetur daga Najeriya na watan da ya wuce su na nan jibge har yanzu ba a samu wanda zai saya ba. Bincike ya nuna cewa kasuwar man na Najeriya ya soma yin kasa.

Binciken da Energy Information Administration tayi ya tabbatar da cewa kasuwar irin su Najeriya da kasar Angola ya fara yin kasa ne tun bayan da Amurka ta shigo cikin kasashen da su ka fi kowa fitar da man fetur yanzu a Duniya.

A cikin shekarar 2014 da kuma 2015, akwai lokutan da kasar Amurka ta daina sayen man fetur gaba daya daga hannun Najeriya. An dai taki sa’a, gangar man fetur ya kara kudi a Duniya bayan wani juyi da aka samu a cikin shekarar 2018.

Asali: Legit.ng

Online view pixel