Rikita-rikita: Gwamnonin APC na shirya kullalliyar tsige Gwamna Okorocha

Rikita-rikita: Gwamnonin APC na shirya kullalliyar tsige Gwamna Okorocha

Da alama dai tsugune bata kare ba a rikicin da ake cigaba da tafkawa a tsakanin 'ya'yan jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) biyo bayan bankado wani shiri da gwamnonin jam'iyyar keyi na tsige gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a matsayin shugaban kungiyar su.

Majiyar mu ta Daily Independent dai ta samu labarin cewa tuni maganar cire gwamnan tayi karfi a tsakanin gwamnonin musamman ma ganin cewa kungiyar ta gwamnonin APC ta jima bata yi taro ba tun bayan sabanin da gwamnan na Imo ya samu da uwar jam'iyya.

Rikita-rikita: Gwamnonin APC na shirya kullalliyar tsige Gwamna Okorocha
Rikita-rikita: Gwamnonin APC na shirya kullalliyar tsige Gwamna Okorocha
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin sunayen 'yan majalisar jihar Katsina

Haka ma dai sauran dalilan da suka sa gwamnonin ke son tsige gwamnan haka zalika sun hada da zargin cin dunduniyar jam'iyyar da yayi wajen kin goyon bayan dan takarar ta a zaben gwamnan da ya gudana da ake ganin shine musabbabin faduwar jam'iyyar zaben jihar.

Tuni dai binciken na majiyar mu ya bankado kulle-kullen da ake yi na baiwa gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi rikon kwarya na kungiyar gwamnonin kafin zabe.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai jam'iyyar ta APC a matakin kasa ta dakatar da gwamnan na Imo da na Ogun bisa zargin yi masu zagon kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel