Maimaita zabe a Kano: Ku zargi Kwankwaso idan aka samu tashin hankali - APC

Maimaita zabe a Kano: Ku zargi Kwankwaso idan aka samu tashin hankali - APC

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano ta bukaci hukumomin tsaro da al'ummar Jihar Kano su zargi Sanata Rabi Musa Kwankwaso idan aka samu wani tashin hankali kafin zabe, lokacin zabe da bayan zaben gwamna da za a gudanar a ranar 23 ga watan Maris a jihar.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan watsa labarai, Matasa da Al'adu wanda kuma shine shugaban kwamitin yakin neman zaben APC a Kano, Malam Muhammad Garba ya ce shugabanin APC na jihar sun damu matuka game da kalaman da aka ce Kwankwaso ya furta kuma yana mamakin yadda hukumomin tsaro ja masa kunne ba.

Ya ce, "Kowa ya san yadda Sanata Rabiu Kwankwaso ya dauki zaben da za a maimaita a Kano a ranar 23 ga watan Maris tamkar yaki da bai shirya shan kaye ba. Kalaman da ya furta a baya-bayan nan na nuna cewa yana iya tayar da rikici a jihar Kano kafin zabe, lokacin zabe da bayan zabe."

DUBA WANNAN: Banbarakwai: Alkalin Alkalai, Walter Onnoghen da aka dakatar ya bayyana a gaban kotu

Maimaita zabe a Kano: Ku zargi Kwankwaso idan aka samu tashin hankali - APC
Maimaita zabe a Kano: Ku zargi Kwankwaso idan aka samu tashin hankali - APC
Asali: Depositphotos

"Akwai hujoji da ke nuna cewa Sanata Kwankwaso yana cigaba da amfani da magoya bayansa wurin tayar da rikici da razana al'umma a sassa daban-daban na Kano duk da cewa ba shine dan takarar gwamna na jam'iyyar ba."

Sanarwar ta cigaba da cewa, "a matsayin mu na jam'iyya mai biyaya da doka da oda, APC ba ta dauki zabe a matsayin harkar a mutu ko ayi rai ba. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shugaba ne mai son zaman lafiya kuma ba zai so a zubar da jinin al'umma saboda zabe ba.

"Gwamna Ganduje ya yi imanin cewa Allah ne ke bayar da mulki kuma shi ke karbe mulkin. Ayyukan cigaba da ya gudanar a jihar sun isa su bashi nasara.

"Muna kira ga masu ruwa da tsaki a harkar da su sanya baki domin kiyaye afkuwar tashin hankali, tun hawar Ganduje mulki ya cigaba da kiyaye zaman lafiya a jihar. Mun dade muna zaune lafiya kuma ba zamu amince wasu su zo su kawo mana tashin hankali saboda son zuciya ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel