Najeriya na kashe Dala miliyan 500 wajen shigo da man ja duk shekara - CBN

Najeriya na kashe Dala miliyan 500 wajen shigo da man ja duk shekara - CBN

Mista Godwin Emefiele, shugaban babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya bayyana cewa 'yan Najeriya na kashe kudaden da suka kai akalla Dalar Amurka miliyan dari biyar a duk shekara wajen shigo da man ja daga kasashen waje.

Shugaban Central Bank of Nigeria (CBN) din yayi wannan ikirarin ranar Litinin din da ta gabata da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na masu sana'ar man ja a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Najeriya na kashe Dala miliyan 500 wajen shigo da man ja duk shekara - CBN
Najeriya na kashe Dala miliyan 500 wajen shigo da man ja duk shekara - CBN
Asali: UGC

KU KARANTA: Akpabio ya garzaya kotu kan zaben da ya sha kaye

Taron dai kamar yadda muka samu ya samu halartar gwamnonin jahohin Akwa Ibom, Edo da Abiya. Haka ma shugabanni daga kamfanonin 'yan kasuwa kamar su Dangote, Flour Mills, United Food Industries da ma Dufil Prima Foods Plc dukkan su sun halarci taron.

Mista Emefiele ya bayyana takaicin sa akan yadda kasa kamar Najeriya ke cigaba da shigo da man jan duk kuwa da irin albarkar sa da Allah ya zuwa a kasar.

Ya kara da cewa hakan tamkar girman banza ne ga kasar wadda a shekarun baya can ita ce tafi kowace kasa a duniya man jan kuma ma har kasashe kamar su Indonisia da Maleysiya a wurin Najeriya suka amshi irin kwakwar man ja amma yanzu sun fi mu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel