Gwamnati za ta fara jigilar kaya daga tashar ruwa na Legas zuwa Kaduna a jirgin kasa

Gwamnati za ta fara jigilar kaya daga tashar ruwa na Legas zuwa Kaduna a jirgin kasa

Gwamnatin Najeriya ta kammala duk wasu shirye shirye da tsare tsaren fara kwaso kaya daga tashashohin jiragen ruwa dake jahar Legas zuwa tashar jirgin ruwa na kan tudu dake jahar Kaduna daga ranar 16 ga wata Afrilun bana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnati zata fara jigilar kayan ta hanyar amfani da sabbin taragogin jirgin kasa guda ashirin da hudu data sayo domin rage ma yan kasuwa wahalhalun da suke fuskanta wajen shigo da kayayyaki.

KU KARANTA: Mutane 8 sun mutu a sanadiyyar bamabaman da Boko Haram ta binne akan hanya

Shugaban hukumar kula da sufurin jirgin ruwa ta Najeriya, Hassan Bello ne ya bayyana haka, inda yace sun hada kai da hukumar kula da sufurin jirgin kasa ta Najeriya, wanda ta samar da taragogin daukan kayan guda 24.

“Yanzunan muka gudanar da tattaunawa da hukumar kula da sufurin jirgin kasa ta Najeriya, kuma zuwa yanzu mun samar da tarago 24 na daukan kaya daga tashoshin jirgin ruwa dake Legas zuwa tashar kan tudu ta Kaduna.” Inji shi.

Haka zalika Bello ya tabbatar da cewa zasu yi aiki sosai sakamakon tashoshin jiragen Najeriya sun gyaru, kuma sama da kashi 80 na jiragen ruwan dake shigowa yammacin Afirka a Najeriya suke tsayawa, kuma nan bada jimawa ba jiragen ruwa zasu fara kai kaya yankin kudu masu gabashin kasarnan.

Idan za’a tuna a shekarar data gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar jirgin ruwa ta kan tudu dake unguwar Kakuri ta jahar Kaduna, tashar da aka ginata da nufin saukaka ma yan kasuwa shige da fice kayayyakinsu, kuma an hadata da layin dogo da kuma babban titi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel