‘Yan daba sun kashe mutane da-dama a babbar Poly da ke Jihar Imo

‘Yan daba sun kashe mutane da-dama a babbar Poly da ke Jihar Imo

Akalla mutane 10 ne su ka rasa rayukan su a sanadiyyar wani rikici da ya barke tsakanin wasu kungiyoyin asiri. Mafi yawan wadanda su ka rasu, dalibai ne kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto mana.

A Ranar Lahadin nan ne rigima ta kaure tsakanin wata kungiya da ake kira Ayes da kuma kungiyar Baggers confraternities. An dai dauki kusan kwanaki 10 cur ana wannan mummunan rikici wanda ya sa jama’a da dama su ka tsere.

Kamar yadda wani 'Dalibi ya fadawa ‘yan jarida, mutanen yankin sun tsere daga Unguwar ne a dalilin wannan rigima da tayi kamari, rikicin ya kuma jawo an tsaida karatun boko da ake yi a wata makarantar gaba da Sakandare.

Tuni dai hukumar makarantar tarayayyar ta Polytechnic da ke Nekede ta maka dokar ta baci inda aka hana ‘dalibai yawo bayan karfe 6:00 na yamma. Wasu ‘Daliban makarantar sun ce rikicin da aka yi wannan karo yayi kazamin muni.

KU KARANTA: Mutane 8 sun mutu a sanadiyyar bama-baman Boko Haram

‘Yan daba sun kashe mutane da-dama a babbar Poly da ke Jihar Imo
Rigima ta kaure tsakanin wasu ‘yan daba a Jihar Imo
Asali: Twitter

Wani ‘dalibi ya fadawa ‘yan jarida cewa akwia bukatar a kawo ‘yan sanda da jami’an tsaro cikin makarantar domin rigimar da wadannan kungiyoyi na daba su ke yi, yayi kamari inda ake kashe Bayin Allah kamar kiyashi a garin.

Ana yin wannan rikici ne a cikin Garin Umudibia Nekede da ke jihar Imo. Hakan ya sa jama’a da dama sun gaza fitowa daga cikin gidajen su, inda kullum su ke boye a cikin gida saboda gudun a harbe su har lahira ba tare da dalili ba.

Shugaban wannan makaranta da ke Nekede watau Martin Aligbe yace rikicin bai shafi ‘daliban sa ba, Yanzu dai jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargi da hannu da wannan mugun aiki. Irin wannan rikici dai ya zama ruwan dare.

Daga cikin wadanda ‘yan sanda su ka cafke akwai: Kalu Chibueze, Obinna Ojike, Amadi Nnaemeka, Iwuagwu Martins, Chiamaka John, Nnesoma John, Kingsley Nwogu, da kuma wani Uche Chimebere.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel