Mutane 8 sun mutu a sanadiyyar bamabaman da Boko Haram ta binne akan hanya

Mutane 8 sun mutu a sanadiyyar bamabaman da Boko Haram ta binne akan hanya

Mutuwa dayace, amma sababinta da dama, wannan shine kwatankwacin lamarin daya faru a karamar hukumar Gwoza ta jahar Adamawa, inda wasu bamabamai da mayakan Boko Haram suka binne akan hanya suka tashi da mutane takwas.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne a kauyen Warabe dake nisan kilomita 15 daga garin Gwoza, inda wata mota dake dauke da mutanen takwas ta bi ta kan bamabaman a cikin rashin sani, inda nan take bamabaman suka tashi motar, duka mutane 8 suka mutu.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kaddamar da mummunan hari a Adamawa, sun kona banki

Motar na cikin jerin ayarin motocin fararen hula ne wadanda Sojoji ke yi ma rakiya zuwa garin Pulka, amma sai direban motar ya sauka daga kan titi da nufin tsere ma motar dake gabansa, saukarsa daga hanya keda wuya ya bi ta kan bamabaman dake binne a gefen hanya.

Wani jami’in Soja ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace mayakan Boko Haram ne suka binne bamabaman da nufin jefa rayuwar mutanen karkara cikin hadari, kamar yadda suke yi a sauran kauyukan jahar Borno.

“Motar ta fashe gaba daya, kuma duka jama’an dake cikinta su takwas sub mutu murus, yayin da wasu mutane bakwai dake cikin motoci na daban suka samu munanan rauni.” Inji jami’in Sojan.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa wannan ba abin mamaki bane sakamakon yan ta’addan dake karkashin jagorancin Abubakar Shekau sun mamaye yankin, domin kuwa ko a watan data gabata sun jefa bom cikin Masallaci wanda ya kashe mutane uku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel