Yaki da rashawa: An sallami jami’an Yansanda 3 saboda karbar cin hancin N1,810,000

Yaki da rashawa: An sallami jami’an Yansanda 3 saboda karbar cin hancin N1,810,000

Kotun dake shiga tsakanin ma’aikatan gwamnati da gwamnati ta tabbatar da sallamar da rundunar Yansandan Najeriya tayi ma wasu jami’anta guda uku bayan ta kamasu da laifin karbar cin hancin dala dubu biyar, kimanin naira miliyan daya da dubu dari takwas kenan, inda tace matakin yayi daidai.

Yansandan da matakin sallamar ya shafa sun hada da sufeta Joseph Okan, sufeta Joshuwa Madame da sajan Cyprian Nwankwo, amma sai basu hakura ba suka garzaya gaban kotun inda suka kalubalanci babban sufetan Yansanda daya koresu, tare da neman ta mayar dasu bakin aikinsu.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kaddamar da mummunan hari a Adamawa, sun kona banki

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Rakiya Haastrup ta bayyana cewa Yansandan sun shaida ma kotu cewa ba’a bi ka’ida ba wajen sallamar tasu, sai dai Alkali Rakiya tace Yansandan sun gagara bayyana mata takardun daukansu aiki.

“Duk da hujjojin da masu kara suka bayyana ma kotu, amma sun gaza bayyana ma kotu shaidar daukansu aiki balle ma kotu ta san dokoki da yarjejeniyar aikinsu da hukumar Yansanda, don haka kotu ba zata iya tabbatar da karya doka daga bangaren hukumar Yansanda ba.

“Doka ta tanadar da cewa duk wanda ya shigar da karar an sallameshi daga aiki, lallai sai ya tabbatar da hujjar daukansa aiki tun daga farko, ta haka ne kawai za’a iya kwatar masa hakkinsa, don haka masu kara basu da wani hujja a idon sharia.” Inji ta.

Da fari dai lauyan Yansandan guda uku, Ginika Chinemere ta nemi kotu ta haramta matakin da hukumar Yansanda ta dauka na sallamarsu, ta mayar dasu baki aiki, ta biyasu albashinsu da alawus alawus dinsu tun daga lokacin data sallamesu, sa’annan ta biyasu diyyar naira miliyan 500.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel