2019: Abin da ya sa Gbenga Daniel yake neman tserewa daga PDP

2019: Abin da ya sa Gbenga Daniel yake neman tserewa daga PDP

Darekta Janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP watau Gbenga Daniel, ya sanar da cewa yayi murabus daga tafiyar jam’iyyar adawa ta PDP, kuma ya ajiye siyasa a gefe guda.

Sahara Reporters ta bi diddiki ta kawo dalilan da ake gani, su ne su ka tunzura tsohon gwamnan ya tsere daga jam’iyyar ta PDP. Gbenga Daniel yana ganin cewa ba a damawa da shi a PDP tun da Atiku ya samu tikin takarar 2019.

Daga cikin abubuwan da su ka Gbenga Daniel ya fice daga PDP akwai hana sa kujerar shugaban jam’iyya da aka yi. Daniel yana cikin wadanda su kayi harin shugaban PDP, wanda a karshe aka dauke ta kaf daga kasar Yarbawa.

KU KARANTA: INEC ta hana Gwamnan APC takardar nasara bayan ya ci zaben Sanata

2019: Abin da ya sa Gbenga Daniel yake neman tserewa daga PDP
Tsohon gwamnan Ogun Gbenga Daniel yana neman komawa APC
Asali: UGC

Gbenga Daniel shi ne yayi wa Atiku Abubakar yakin samun tikitin shugaban kasa a PDP, amma ana zargin cewa PDP ta maida Gbenga Daniel saniyar ware bayan Atiku ya samu takara inda aka maye gurbin sa da Bukola Saraki.

Rikicin PDP tsakanin Obasanjo-Kashamu, da kuma rigimar Kashamu da Adebutu a Ogun yana cikin abin da ya sa tsohon gwamnan ya fice daga jam’iyyar. Wannan rikici dai ya jawowa PDP matsala a jihar a zaben 2019 ana ji ana gani.

Tsohon gwamnan na Ogun, Gbenga Daniel yana ganin cewa akwai wani boyayyen shiri da ake yi na kauda Yarbawa daga cikin jam’iyyar PDP. Babu mamaki hakan ya sa ya tattara ya bar jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel