Mayakan Boko Haram sun kaddamar da mummunan hari a Adamawa, sun kona banki

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da mummunan hari a Adamawa, sun kona banki

Kungiyar ta’addanci ta mayakan Boko Haram sun kaddamar da wata mummunan hari a kokarinsu na afkawa cikin garin Michika na jahar Adamawa tare da kokarin karbe garin, sai dai sun samu tirjiya daga dakarun rundunar Sojin kasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mazauna garin Michika sun bayyana cewa da misalin karfe 7 na daren jiya suka fara jin karar harbe harbe daga kan hanyar Michika zuwa Lasa, daidai lokacin da Sojoji suke shan artabu da yan Boko Haram kenan.

KU KARANTA: Zaben Gwamnan Kano: Kwamishina ‘Maza kwaya Mata kwaya’ ya kai ma Malaman Darika ziyara

Shima wani mazaunin kauyen Bazza dake kusa da garin Michika, John Jigalambu ya tabbatar da aukuwar harin, inda yace daga kauyensu suna jiyo karar musayar wuta tsakanin mayakan Boko Haram da Sojoji, hakan tasa kafatanin jama’an kauyen tserewa.

Kwamishinan watsa labaru na jahar Adamawa, Ahmad Sajoh ya tabbatar da harin da mayakan kungiyar ta’addancin suka ka, sai dai ya bayyana cewa Sojoji na iya bakin kokarinsu don ganin sun wartaki mayakan na Boko Haram.

Kwamishina Sajoh ya kara da cewa yan ta’addan sun shiga garin Michika ne daga kauyen Kirchinga dake cikin karamar hukumar Madagali, sa’annan ya cigaba da fadin cewa sun kona bankin First Bank da wasu shaguna, amma dai Sojoji sun samu nasarar fatattakarsu.

A wani labarin kuma, Wata karamar yarinya mai shekaru goma sha uku mai suna Zara, wanda mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka tilasta mata kai harin kunar bakin wake ta hanyar daura mata bamabamai a jikinta, ta shiga hannun matasan Sojojin sa kai a jahar Borno.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel