Hadi Sirika yace CP Wakili ya cancanci ya zama Gwarzon shekara a Najeriys

Hadi Sirika yace CP Wakili ya cancanci ya zama Gwarzon shekara a Najeriys

Ministan sufurin harkokin jirgin saman Najeriya, Sanata Hadi Sirika yana cikin wadanda su ka yaba da aikin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano, CP Mohammed Wakili wanda ake kira Singham.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne ake ta yabawa irin aikin da Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Wakili Mohammed, yayi wajen ganin an gujewa tarzoma a zaben gwamna da aka yi. Hadi Sirika yana cikin masu yabon na sa.

Ministan na harkokin jirgin saman kasar ya jinjinawa babban jami’in ‘yan sandan na jihar Kano a shafin sa na sadarwa na Tuwita. Kayode Ogundamisi, shi ne ya fara kawo maganar M. Wakili, inda yace ya cancanci lambar yabo.

KU KARANTA:Ina ganin mutuncin Kwamishinan ‘Yan Sanda - Kwankwaso

Hadi Sirika yace CP Wakili ya cancanci ya zama Gwarzon shekara
Ministan jiragen sama Hadi Sirika ya yabi CP Singham na Kano
Asali: Facebook

Mista Ogundamisi, a shafin na sa yake cewa Mohammed Wakili ya dace ya zama Gwarzon shekarar 2019, duk da cewa watanni 3 rak aka ci a cikin shekarar ta bana, Ogudamisi yana ganin da wuya a samu wanda zai doke CP.

Hadi Sirika ya maida martani inda yace ya amince 100 bisa 100 cewa Mohammed Wakili ya cancanta da ya zama Gwazon 2019. Hakan dai na nufin cewa Ministan ya sabawa Jam’iyyar sa ta APC da ke zargin Kwamishinan da son-kai,

Jam’iyyar APC mai mulki tana ganin cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan na jihar Kano ya nuna son rai wajen aikin sa inda yake kyale Mabiya jam’iyyar PDP su ke yin abin da su ka ga dama a Kano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel