Maimaita zabe: sai dai fa kowa ta sa ta fishe shi – Buhari

Maimaita zabe: sai dai fa kowa ta sa ta fishe shi – Buhari

A jiya, Lahadi, ne fadar shugaban kasa ta gargadi ‘yan siyasa a kan yin kalaman da kan iya tunzura jama’a gabanin zabukan da za a maimata a wasu jihohi 6 ranar Asabar, 23 ga wata, mai zuwa.

A jawabin da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ya bayyana cewar hukumar zabe ta kasa (INEC) ce keda alhakin tattauna tare da gudanar da duk wasu harkokin zabe, ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Jawabin ya kara da cewa; “wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC na tsammanin shugaba Buhari zai taka doka ta hanyar tsoma baki a batun zabukan da za a maimiata a wasu jihohi, sai dai muna son sanar da su cewar sai dai ‘kowa ta sa ta fishe shi’ don shugaba ba zai nemi a saba ka’ida saboda ‘yan takarar jam’iyyar APC ba.

Sai dai duk da wannan tabbaci da fadar shugaban kasa ta bayar, sai ga shi babbar jami'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ce kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cewar ba zai saka baki a zabukan da za a maimaita a wasu jihohi ba sun tabbatar da cewar ya yarda an tafka magudin zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Maimaita zabe: sai dai fa kowa ta sa ta fishe shi – Buhari
Buhari
Asali: Depositphotos

PDP ta bayyana cewar kalaman na shugaba Buhari wani salo ne na janye hankalin jama'a daga magudin da jam'iyyar APC ke shiryawa a zaben da za a yi a jihohi 6 ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Ganduje: Dakta Baffa Bichi na APC ya ziyarci Abba Gida-gida har gida

Jam'iyyar PDP na wannan kalamai ne a cikin wani jawabi da Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai, ya fitar a yau, Litinin.

Ologbondiyan ya kara da cewa kalaman Buhari dake bayyana cewar wasu mambobin APC na matsa ma sa lamba kan ya sa baki domin a yiwa 'yan takarar ta alfarma ya isa jama'a su fahimci yadda jam'iyyar ta kware a bangaren tafka magudin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel