Yadda ‘yan sandan gwamna Wike su ka ci mutuncin mu tare da raunata mu

Yadda ‘yan sandan gwamna Wike su ka ci mutuncin mu tare da raunata mu

Wasu dakarun rundunar soji guda biyu dake zaman jinya sakamakon rikicin da aka yi a jihar Ribas a zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki sun bayyana yadda wasu ‘yan sandan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, suka lakada ma su duka tare da jikkata su.

A jiya, Lahadi, ne kakakin rundunar soji ta 6 dake Fatakwal, Kanal Aminu Iliyasu, ya tabbatar da sahihancin wani faifafan bidiyo da jami’an sojin ke bayyana yadda aka ci mutuncinsu yayin rikicin da ya barke lokacin zaben.

Sojojin biyu; Kaftin Adams Salami da kofral Adeosun, dake zaman jinya a asibitin koyar wa na jami’ar Fatakwal sun bayyana yadda aka kai masu hari a cibiyar tattara sakamakon zabe dake karamar hukumar Obio/Akpor.

A cewar kaftin Salami; “da misalign karfe 1:00 na rana mun ziyarci zuwa cibiyar tattara sakamako ta Obio/Akpor bayan samun labarin cewar wasu ‘yan ta’adda sun kai hari cibiyar. Bayan mun isa wurin sai muka sa dokar cewar za a takaita shige da ficen jama’a a cibiyar.

Yadda ‘yan sandan gwamna Wike su ka ci mutuncin mu tare da raunata mu
Yadda ‘yan sandan gwamna Wike su ka ci mutuncin mu tare da raunata mu
Asali: Twitter

Minti biyar bayan zuwan mu sai ga tawagar gwamna Nyesom Wike da motoci 30 zuwa 40 cike da ‘yan ta’adda da ‘yan dabar siyasa; wasu daga cikinsu na sanye da kayan ‘yan sanda sun a harbin iska a harabar wurin. Ganin haka ya sa mu ka koma gefe tare da kokarin ganin an warware matsalar cikin ruwan sanyi.”

DUBA WANNAN: Maza na daf da kare wa a duniya – Binciken kimiyya

Kofral Adebayo ya kara da cewa; “a daidai lokacin da muke kokararin shawo kan dandazon jama’ar da gwamnan ya shigo da su cibiyar ne sai wasu ‘yan sanda daga cikin tawagar sa suka fara dukan mu da makamai daban-daban ba tare da wani dalili ba. ‘Yan sandan sun yi amfani da gindin bindigar su sun doke mu, lamarin da ya kai ga sun ji ma na raunuka.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel