Ka san duk magudin da APC ke shirya wa, PDP ta kafa hujja da kalaman Buhari

Ka san duk magudin da APC ke shirya wa, PDP ta kafa hujja da kalaman Buhari

Babbar jami'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ce kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cewar ba zai saka baki a zabukan da za a maimaita a wasu jihohi ba sun tabbatar da cewar ya yarda an tafka magudin zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

PDP ta bayyana cewar kalaman na shugaba Buhari wani salo ne na janye hankalin jama'a daga magudin da jam'iyyar APC ke shiryawa a zaben da za a yi a jihohi 6 ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Jam'iyyar PDP na wannan kalamai ne a cikin wani jawabi da Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai, ya fitar a yau, Litinin.

Ologbondiyan ya kara da cewa kalaman Buhari dake bayyana cewar wasu mambobin APC na matsa ma sa lamba kan ya sa baki domin a yiwa 'yan takarar ta alfarma ya isa jama'a su fahimci yadda jam'iyyar ta kware a bangaren tafka magudin zabe.

Kalaman ka a kan zabukan da za a maimaita sun tabbatar da an yi magudin a zaben shugaban kasa - PDP ta fada wa Buhari
Kola Ologbondiyan
Asali: Twitter

"Idan 'yan Najeriya basu manta ba gabanin zaben shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya, shugaba Buhari ya dauki alkawarin za a yi zabe sahihi na gaskiya amma sai ga shi jagororin jami'iyyar APC sun yi amfani da 'yan daba da jami'an tsaro domin hana jama'a fito wa su kada kuri'a a yankunan da basu da yawan magoya baya.

DUBA WANNAN: Ganduje: Dakta Baffa Bichi na APC ya ziyarci Abba Gida-gida har gida

"Shugaba Buhari ba zai iya wanke kan sa daga zargin magudi ba domin mun san cewar babu wanda yake bawa sojoji umarni sai shugaban kasa," a cewar Ologbondiyan.

Kazalika, PDP ta yi kira ga dakarun soji da su nesanta kan su daga wuraren zabe tare da jan hankalin hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta tabbatar ta bawa jama'a abinda suka zaba musamman a jihohin da PDP ta bawa APC tazarar kuri'u.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel